An kama tsoffin Ministoci 3 na Burkina Faso
A kasar Burkina Faso an cafke wasu tsoffin ministoci uku na gwmanatin tsohon shugaban kasar Blaise Campaore, abin da ya haifar da tada Jijiyoyin Wuya a tsakanin ‘yan siyasar kasar
Wallafawa ranar:
Jam’iyyar tsohon shugaban dai ta bayyana matakin da Hukumomin kasar suka dauka a matsayin tursasawa ga magoya bayanta.
Rahotanni sun ce an cafke mutanen uku ne bisa zargin cewa suna shirya tayar da tarzoma a cikin kasar.
Akasarin mazauna birnin Wagadugu kamar Malam Abubakar Gambo, na ganin cewar al’umma ba su yi mamakin kama wadannan mutane ba, musamman lura da yadda Hukumomin kasar ke tursasawa jam’iyyun adawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu