Burkina Faso
Jam’iyyar adawa a Burkina Faso ta yi yaji kan batun tsayawa takara
Jam’iyyar tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ta ce ba za ta goyi bayan yunkurin da ake na hana ma ta tsayar da ‘yan takara a zabubukan da za a gudanar nan gaba a kasar
Wallafawa ranar:
Talla
A yau talata ne dai Majalisar dokokin rikon kwarya ta kasar za ta yi zama domin tabbatar da hakan, ta hanyar bayyana cewa duk wanda ya taba rike mukami a gwmanatin Campaore to ba zai tsaya takara a zaben ba.
Matsalar nuna banbanci a tsakanin ‘yan Siyasa a Nahiyar Afruka dai matsala ce da ta zama ruwan dare kuma akasari hakan ne ke haddasa tashe-tashen hankullan Siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu