Isa ga babban shafi
Burundi

Sojojin Burundi na neman hadin kan juna

Sabon Ministan tsaron Burundi da babban hafsan Sojan kasar sun nemi hadin kan dakarun kasar, tare da yin kira ga Sojojin da suka nemi hambarar da shugaba Nkurunziza su zo a tafi tare. Wannan na zuwa ne a yayin da rikicin kasar ke ci gaba da zafafa.

An shafe makwanni ana Zangar-zangar adawa da matakin shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza na neman wa'adin shugabanci na uku.
An shafe makwanni ana Zangar-zangar adawa da matakin shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza na neman wa'adin shugabanci na uku. Burundi
Talla

A cikin wata sanarwa sabon Ministan tsaro Emmanuel Ntahonvukiye, ya ce akwai bukatar a tattauna tsakanin Sojojin da ke tafiyar da tsaro a Bujumbura babban birnin kasar.

Rikicin kasar Burundi dai na ci gaba da zafafa, yayin da rahotanni ke cewa ‘yan sandan kasar sun harba harsashe da hayaki mai sa kwalla domin tarwasa masu zanga-zangar adawa da matakin shugaba Nkurunziza na neman wa’adi na uku.

Rahotanni kuma na cewa rikicin Burundi ya koma tsakanin Sojojin da ke biyayya ga gwamnati da kuma bangaren wadanda suka jagoranci juyin mulki a makon jiya.

A jiya Laraba, wani dan sanda ya harbe wani soja har lahira, lamarin da ke kara haifar tsoro da fargaba tsakanin al’umar kasar na rikidewar rikicin siyasar kasar zuwa yakin basasa.

Akan haka ne Ma’aikatar tsaron kasar ke neman hadin Sojoji domin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.