Kotun Masar ta daure Morsi shekaru 20
Kotun kasar Masar ta yankewa hambararen shugaba Mohammed Morsi hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari kan tuhumar da ake ma sa na tinzira jama’a a tashin hankali da ya faru a zamanin mulkinsa a 2012 a cikin kasar. Amma kotun ta wanke Morsi daga tuhumar kisan masu zanga-zanga wanda zai kai a yanke masa hukuncin kisa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotun ta yanke wa hambararren shugaban Mohammed Morsi hukuncin daurin shekaru 20 akan laifin bayar da umurnin a kame masu zanga-zanga tare da gana masu azaba a lokacin da ake zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa a 2012.
Baya ga Morsi Akwai kuma wasu mutane 14 da kotun ta yanke wa hukunci.
Sai dai kuma kotun ta wanke morsi daga laifin da ya shafi bayar da umurnin kisan masu zanga-zanga, wanda zai kai ga yanke masa hukuncin kisa.
Sannan kotun kuma na zarginsa da mika bayanan sirrin gwamnati ga kungiyar Hamas ta Falasdinawa, zargin da zai sa a sake yanke masa wani hukunci
Morsi dai shi ne zababben shugaban kasa na farko a Masar wanda ya gaji gwamnatin Hosni Mubarak da aka hambarar da gwamnatinsa a 2011.
Yanzu haka kungiyar ‘yan uwa musulmi ta kira babbar zanga-zanga domin nuna goyon baya ga Morsi.
Morsi na da ‘yancin daukaka kara bayan kotun ta yanke masa hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu