Boko Haram: An Umurci Sojojin Canada su fice Diffa
Ma’aikatar tsaron Canada ta umurci dakarunta na musamman da ke ba Sojojin Nijar horo akan su fice daga yankin Diffa da ke kusa da kan iyaka da Najeriya saboda barazanar Boko Haram. Sai a watan Maris ne Sojojin za su kammala aikin amma Ma’aikatar tsaro ta bayyana fargaba akan Mayakan Boko Haram na iya abkawa Sojojin.
Wallafawa ranar:
Sojin na Canada suna cikin rundunar sojin kasashe 19 na hadin guiwa karkashin jagorancin Amurka da ke aikin bayar da horo ga sojojin kasashen Afrika guda biyar.
Ma’aikatar tsaron tace an rarraba Sojojin zuwa Agadez da Yamai a Nijar da kuma garin N’Djamena na Chadi a cikin wani sakon Email da ta aikawa kamfanin Dillacin Labaran Faransa,
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu