Isa ga babban shafi
Nijar-Najeriya

An fara raba abinci ga ‘Yan gudun hijira a Diffa

Hukumar bayar da agajin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fara raba wa ‘Yan gudun hijirar Najeriya taimakon abinci a garin Diffa na Nijar bayan dakatar da aikin saboda barazanar hare haren Boko Haram a yankin.

'Yan gudun Hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram
'Yan gudun Hijira da suka tserewa rikicin Boko Haram REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hukumar ta fara raba abinci ga ‘Yan gudun hijirar tun a jiya Laraba bayan dakatar da bayar da agajin a watan jiya saboda barazanar Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Nijar.

Hukumar tace za ta ba sabbin ‘Yan gudun Hijira 37,000 agajin abinci wadanda suka tsallako zuwa Nijar daga Jihohin Yobe da Borno na Najeriya

Sama da mutanen Najeriya 120,000 suka tsallako zuwa Nijar domin tsira daga hare haren Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.