Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram: An yi wa masu fataucin Kifi ruwan wuta a Nijar

Rahotanni daga Janhuriyar Nijar sun ce jirgin yakin kasar ya kai hari kan tawagar ‘yan kasuwar da ke fataucin kifi tsakanin Najeriya da kasar saboda zargin da ake mu su na tallafawa kungiyar Boko Haram da kudade. Wata majiyar sojin kasar ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewar fasinjojin sun yi nasarar tserewa zuwa cikin Najeriya bayan da aka kai hari kan motocinsu.

Sojojin Nijar da ke fada da  Boko Haram a Bosso
Sojojin Nijar da ke fada da Boko Haram a Bosso RFI/Madjiasra Nako
Talla

Kasar Nijar na zargin ‘yan kasuwan da biyan haraji ga kungiyar Boko Haram wadanda ke yi ma su barazanar kwace kifin don sayarwa su samu kudade.

Nijar dai na fuskantar barazanar Boko Haram ne a yankin Diffa da ke makwabtaka da Najeriya.

Tuni kuma Nijar da Kamaru da Chadi da ke bakwabta da Najeriya suka kaddamar da yaki domin kawo karshen Mayakan Boko Haram da ke yin barazana ga kasashen na yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.