Isa ga babban shafi
Libya-Faransa

Hollande yace Faransa ba zata shiga rikicin kasar Libya ba

Shugaban Faransa Francois Hollande yace kasarsa Faransa ba zata shiga rikicin Libya ba ita kadai, tare yin kira ga kasashen duniya su dauki matakan gaggawa domin kawo karshen rikicin kasar. Cikin watat tattaunawa, Shugaba Francois Hollande ya shaidawa Rediyon Faransa cewa Faransa ba zata shiga rikicin kasar Libya ba ita kadai, sai dai tare da goyon bayan wasu kasashen duniya, inda yayi kira ga kasashen duniya su gaggauta daukar matakan da suka dace domin kawo karshen rikicin kasar.kalaman shugaban na zuwa ne a yayin da daya bangaren gwamnatin Libya da ke samun goyon bayan kasashe duniya ya yi kira ga kasashe su taimaka da makamai domin yakar mayakan Sa-kai da suka kwace wasu yankunan kasar.Tuni dai shugaban kasar Nijar Muhammadu Issoufou da ke makwabtaa da Libya ya bayyana cewa sai kasashen duniya sun sa hannu domin kawo karshen rikicin kasar.Kasar Libya dai ta shiga rudani ne tun kawo karshen gwamnatin Kanal Gaddafi, inda mayakan sa-kai masu da’war Shari’a ke gwagwarmayar kafa gwamnati duk da sabuwar gwamnati da aka kafa a kasar.Mayakan da ake kira Fajr Libya su ke rike da ikon Tripoli da Misrata tare da mamaye wani yanki na garin Benghazi. 

Presidente francês François Hollande durante entrevista à rádio France Inter.
Presidente francês François Hollande durante entrevista à rádio France Inter. REUTERS/Remy de la Mauviniere/Pool
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.