Isa ga babban shafi
Kenya

Kenyatta ya amince da dokar yaki da ta’addanci

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya sa hannu kan wata sabuwar dokar yaki da ta’addanci, wacce ta haifar da rudani a zauren majalisar kasar. A jiya Alhamis sai da ‘Yan Majalisa suka ba hamata iska game da amincewa da dokar.

Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta.
Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta. Reuters
Talla

‘Yan adawa dai suna ganin gwamnatin Kenyatta na son komawa ta ‘yan kama-karya.

Yayin da kuma gwamnatin Kenyatta ke cewa tana bukatar dokar domin yakar Mayakan Al Shabaab da ke addabar kasar.

Kenya dai na fama da hare haren Mayakan Al Shabaab na Somalia, lamarin da ya sa gwamnatin Kenyatta ke son daukar matakan tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.