Isa ga babban shafi
Kenya

Kenya ta kori Shugaban ‘Yan sanda

Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya kori Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar da kuma ministan cikin gida a wani mataki da ya danganta na nuna sakaci da aiki da ya sa Mayakan al Shabaab suka kai hari inda suka kashe mutane 36 daren litinin.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta REUTERS/Stringer
Talla

A jawabin da ya yi wa ‘Yan kasa a kafar Telebijin, shugaba Kenyatta ya sha alwashin yaki da ta’addanci a kasar.

A ranar Litinin ne Mayakan Shabaab suka kai hari a garin Mandera tare da kashe mutane36.

Tuni dai Mayakan Shabaab suka ce sun kaddamar da hare hare ne a Kenya domin mayar da martani ga matakin Soji da kasar ta dauka a Somalia da kuma yadda gwamnatin kasar ke cin zarafin musulmi a garin Mombasa.

Rahotanni sun ce gwamnatin Kenya ta tube shugaban ‘yan sandan ne bayan wasu rahotanni da kafafen yada labaran kasar  suka ce an sanar da ‘yan sanda labarin kai wa mata mota kirar bus hari kafin al’amarin ya auku.

Masana suna ganin matakin da Shugaban na Kenya ya dauka ya dace domin hakan zai sa ‘Yan sanda suka kara himmar aiki.

Abubakar Bula Tsav, tsohon kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Lagos a Najeriya yace korar duk wani dan sandan da bai iya aiki ba mataki ne da ya dace.

03:26

Abubakar Bula Tsav, tsohon kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Lagos a Najeriya.

Bashir Ibrahim Idris

Tsav yace irin wannan matakin ne ya kamata a dauka a Najeriya idan ana son yakar Mayakan Boko Haram da ke ci gaba da kisan mutane a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.