Ana tsadar rayuwa a Masar
Mutane Kasar Masar na juyayin halin tabarbarewar tattalin arzikin da ya addabi kasar su abinda ya sa aka samu tsadar rayuwa sabanin yadda akasar take a baya. Rahotanni sun ce kayan abinci da makamashi sun yi tashin goran zabbi inda ‘yan kasar ke cewa gara jiya da yau.
Wallafawa ranar:
Imam Sayeed Inuwa na jami’ar Al Azhar da ke zama a birnin al Kahira yace Talaka yanzu yana mamakin yadda al’amurra suka tarbarbare.
Inuwa wanda yace ya kwashe shekaru 20 a Masar yace a shekarun baya yana da wahala a yi karin farashi a Masar amma lamarin yanzu ya sauya.
Wannan na faruwa ne saboda rikicin siyasa da sauyin gwamnatoci da aka samu a kasar Masar.
A cikin watan Jiya ne Shugaban kasa Abdel Fatah al Sisi wanda ya hambarar da gwamnatin 'Yan Uwa Musulmi ta Mohammed Morsi ya kara fashin Mai, a wani mataki da gwamnatin ta yi ikirarin daidaita tattalin arzikin Masar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu