Dakarun Faransa sun yi gumurzu da ‘Yan Seleka
An yi wani kazamin dauki ba dadi tsakanin dakarun kasar Faransa da tsoffin mayakan yan tawayen kungiyar Saleka a garin Batangafo, da ke yankin arewacin kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, inda rahotani suka bayyana cewa ‘yan tawaye da dama sun rasa rayukansu a cikin fadan.
Wallafawa ranar:
Wani Sojan rundunar tsaro da Afrika MISCA ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa dakarun Faransa sun budewa ‘Yan tawayen Seleka wuta bayan sun abkawa garin Batangafo a ranar Litinin.
Sojan yace ‘Yan tawayen Seleka da dama ne aka kashe a musayar wuta da suka yi da dakarun Faransa.
Hedikwatar dakarun kasar Faransa a birnin Paris ta tabbatar da wannan gumurzu, tare da cewa ‘yan tsageran kungiyar Saleka cike a budaddiyar mota wasu kuma a kan babura suka abkawa dakarun Fransar da manyan makaman yaki.
Faransa dai tace babu ko sojanta da ya rasa ransa ko rauni a harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu