Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Saleka da anti balaka sun amince su tsagaita wuta

Bangarorin da ke rikici a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta don kawo karshen tashin hankalin da suka kwashe shekara guda suna yi wanda ya lakume rayukan jama’a da dama. Bangarorin biyu sun amince da yarjejeniyar zaman lafiyar ne a kasar Congo Brazzaville.

Mayakan sa-kai na Anti-Balaka a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Mayakan sa-kai na Anti-Balaka a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya REUTERS
Talla

Yarjejeniyar ta kunshi wanzar da zaman lafiya a dukkanin sansan yankunan kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

A karkashin yarjejeniyar, kungiyar Seleka ta Musulmi ta janye bukatar ganin an raba kasar tsakanin ta da kungiyar Anti Balaka ta Kirista bayan kashe dubban mutane a rikicin kasar da aka dade ana fafatawa wanda ya tilastawa mutane sama da miliyan hudu da rabi barin gidajensu.

Jagoran kungiyar a taron sasantawar Mohammed Moussa Dhaffane yace sun sanya hannu a gaban kowa kuma za su mutunta yarjejeniyar.

Patrick Edourad Ngaissona shugaban tawagar Anti Balaka ya amince a kama duk wanda aka samu yana karya yarjejeniyar.

Shugaban kasar Congo Denis Sasso Nguesso da ya jagoranci taron ya bayyana farin cikinsa da nasarar da aka samu a tsakanin bangarorin biyu.

Tun a watan Maris ne kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin sabon rikici bayan Mayakan Saleka sun kafa gwamnatin Michel Djotodia, shugaba na farko Musulmi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.