Isa ga babban shafi
jamhuriyar afrika ta tsakiya

Kungiyar ‘yan tawayen Seleka ta ce Djotadia ne shugabanta

Kungiyar Seleka a Jamhuriyar Afruka ta tsakiya ta sake bayyana tsohon shugaban kasar Michael Djotadia a matsayin shugabanta. A shekarar da ta gabata dai Djotadia ne ya jagoranci wannan kungiya da kuma ta kawar da shi daga kan Kargaar mulki

haveeru.com.mv
Talla

Michael Djotadia dai ya sauka daga karagar mulkin kasar ne a Watan Junairu bayan matsin lambar da ya fuskanta daga hukumomin kasa-da-kasa masu cewar Djotadia na jagorantar Kungiyar ta Seleka da suka kira kungiyar ‘yan ta’adda ne.

Tsohon shugaban kasar da ta yi zama a karkashin mulkin mallakar kasar Faransa dai da mataimakinsa a shugabancin kungiyar ta Seleka, na fuskantar Takunkumi ne daga Kasar Amurka da Majalisar dunkin Duniya.

Tun bayan da aka fitar da mambobinta daga birnin Bangui dai Kungiyar ta Seleka ta kasance babbar matsala ga yankin tsakkiya da kuma Arewacin kasar ta Jamhuriyar Afruka ta tsakiya.

Ya zuwa yanzu dai an kwashe fiye da Shekara 1 ana tashin hankali a kasar mai yawan al’umma Miliyan 4.5.

Tashin hankalin ya zama na kule da Cas ne a sakanin Kungiyar Seleka ta musulmin kasar da kuma anti-Balaka ta Kiristocin kasar, kuma akalla Dubban mutane sun mutu a yayin da wasu da dama suka gujewa Gidajensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.