Sabon fada a birnin Bangui na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Sabon rikici ya barke a birnin Bangui na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a daidai lokacin da ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ke soma ziyarar aiki a kasar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce fada ya barke ne tsakanin magoya bayan kungiyar Seleka da kuma Anti-balaka gab da lokacin da ministan ya isa kasar, inda aka tabbatar da mutuwar akalla mutum daya tare da raunata wasu a kusa da wata mujami’a da ke birnin.
Wannan ne dai karo na bakwai da ministan na Faransa ke kai ziyarar aiki a kasar mai fama da rikicin addini da kabilanci, inda jim kadan bayan isarsa a birnin Bangui Le Drian ya ziyarci barikin sojan Mpoko wanda shi ne babban sansanin da daruruwan sojojin Faransa ke amfani da shi a matsayinsu na masu aikin wanzar da tsaro da zaman lafiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu