Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a Bangui

Dubban mutanen kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya sun kaddamar da zanga-zangar kin jin gwamnati tare da neman ficewar dakarun kasashen waje a cikin kasar. Rahotanni sun ce Jami’an tsaro sun harba harsashen bindiga domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Masu zanga-zanga a kasar Jamguriyyar Afrika ta tsakiya
Masu zanga-zanga a kasar Jamguriyyar Afrika ta tsakiya AFP PHOTO / MARCO LONGARI
Talla

Wakilin Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP yace ya ji karar harbin a kusa da filin jirgin saman birnin Bangui, a daidai lokacin da masu zanga zanga suka mamaye titunan birnin.

Wata majiyar Sojan kasar tace matasan kasar suna bore ne domin adawa da matakan da gwamnati ke dauka, tare da neman ficewar sojojin kasashen waje da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

Mutane da dama ne aka ruwaito sun samu rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.