Kungiyar Seleka ta bukaci a raba Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Wakilai fiye da 200 daga bangarori daban daban da ke da hannun a rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne ke halartar taron sulhu wanda aka buda ranar litinin ta wannan mako a birnin Brazaville na kasar Congo.
Wallafawa ranar:
Taron wanda ke gudana a karkashin jagorancin shugaban kasar ta Congo Denis Sasso Nguesso, na samun halartar shugabar rikon kwarya ta Afirka ta Tsakiya Catherine Samba-Panza, da wakilai ‘yan tawayen Seleka da kuma na sauran jam’iyyun siyasa.
Jagoran tawagar ‘yan tawayen Seleka a taron Mohamed Moussa Dhaffane, a cikin wata sanarwa da ya karanta a gaban mahalarta taron, ya bayyana cewa babban bukatarsu ita ce raba kasar domin samun dawwamammen zaman lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu