Algeria
Shugaba Bouteflika zai yi takarar shugabancin kasar Aljeriya
Yau Asabar Priministan kasar Algeria Abdelmalek Sellal, ya ce shugaban kasa Abdelaziz Bouteflika zai yi takarar shugabancin kasar, da za a yi a watan Aprilu mai zuwa. Sellal ya fadi haka ne lokacin da yake hira da manema labaru a yayin wani taron tattalin arzikin kasar da ake yi a birnin Oran, da ke yamma da birnin Algiers.Kafafen yada labarum kasar sun ce gobe Lahadi shugaban, mai shekaru 76 a duniya zai karbi takardun neman tsayawa takarar, da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar.A bara shugaba Bouteflika ya yi fama da ciwon bugun zuciya, inda ya shafe watanni 3 a wani asibitin kasar Faransa.
Wallafawa ranar: