Isa ga babban shafi
Madagascar

Watakila aje zagaye na 2 a zaben shugaban kasar Madagascar

A daidai lokacin da ake ci gaba da fitar da sakamakon zaben shugabancin kasar Madagascar da aka gudanar a jiya, rahotanni na cewa akwai yiyuwar za a je zagaye na biyu na zaben, kafin a samarwa kasar da sabon shugaba. Izuwa tsakiyar daren jiya dai, duka duka sakamakon mazabu 500 ne daga cikin mazabu sama da dubu 20 aka fitar, to amma duk da haka ana ganin cewa za a kara ne a zagaye na biyu tsakanin Robinson Jean-louis da ke samun goyon bayan hambararren shugaban kasar Marc Ravalomanana da kuma Her Radzo na hannun damar shugaban rikon kwarya Andry Rajeolina.Hukumar zaben kasar Cenit, tace za a kai kimanin mako guda kafin a sami cikakken sakamakon karshe na zaben.Sabuwar zababbiyar gwamnati na da muhimmanci a kasar, da ke kan tsibirin tekun Atlantika, a nahiyar Africa, in har kasashen duniya za su ci gaba da bata tallafin da aka dakatar, bayan da Andry Rajoelina ya hambarar da gwamnatin Marc Ravalomanana a shekarar 2009.An haramtawa wa dukkan mutanen 2 shiga takarar wannan zaben, bayan da kasshen duniya suka sanya baki a cikin batun.Kungiyoyin masu sa ido a zaben, da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, sun ce zaben ya gudana cikin nasara, duk da ‘yan matsalolin da aka samu, da suka hada da tashe tashen hankula a wasu yankunan kasar. 

Wasu masu kada kuri'a, a zaben shugaban kasar Madagasca
Wasu masu kada kuri'a, a zaben shugaban kasar Madagasca REUTERS/Thomas Mukoya
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.