Isa ga babban shafi
Madagascar

Rikici ya lafa a Madagascar amma rundunar soji sun kashe shugaban ‘Yan tawaye

Rundunar sojan kasar Madagascar tace an shawo kan boren da wasu sojoji suka ji a jiya lahadi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane Uku. Dakarun Sojin kasar sun ce sun cafke masu boren da dama.

dakarun kasar Madagascar
dakarun kasar Madagascar AFP PHOTO / Andreea Campeanu
Talla

Sojojin sun karbe iko Barikin Soji ne da ke da nisan kilimita 10 da birnin Antananarivo babban birnin kasar.

Har yanzu babu wani bayani game da bukatar masu boren amma rikicin ya samo asali ne bayan da suka bndige wani Jami’in Soji da aka tura domin sasantawa.

Boren na zuwa ne a daidai lokacin da bangarorin kasar, da basa ga maciji da juna ke shirin hawa teburin sasantawa a ranar laraba mai zuwa.

Madagascar ta shiga rikicin siyasar tun bayan da sojoji suka bayar da goyon bayan kifar da gwamnatin Marc Ravalomanana a shekarar 2009.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.