Matan shugabannin Burkina Faso da Cote D’Ivoire sun kaddamar da yaki akan safarar yara
Matan shugabannin kasashen Burkina Faso da kuma Cote D’Ivoire, sun kaddamar da wani shiri domin yaki da matsalar safarar yara kanana da ke ci gaba da yin kamari a tsakanin kasashensu.
Wallafawa ranar:
Chantal Compaore da kuma Dominique Ouattara, sun bayyana aniyarsu ta yaki da wannan matsala a tsakanin kasashen, inda aka ce akalla yara kanana dubu 1,895 ne aka tsallaka iyakokinsu da su a cikin shekarar da ta gabata kawai.
Kasar Cote D’Ivoire ta kasance wani dandali na na safarar yara kanana inda ake shigo da yara kanana daga kasashen Mali da Burkina Faso.
Shirin matan shugabannin a cewar rahotanni zai fadada irin matakan da ake da su a kasa na yaki da wannan matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu