Isa ga babban shafi
Kenya

Dakarun Kenya sun yi ikrarin kwace yankin karshe dake hanun Al Shabab

Rundunar Sojin Kenya ta sanar da kwace sansani na karshe wadda kungiyar Al Shabab ta kasar Somalia ke rike da shi a tashar ruwan Kismayo, abinda ake ganin zai kawo karshen ‘Yan kungiyar a kasar.

Dakarun Kenya a wata fafatawa da su ka yi 'Yan kungiyar Al Shabab.
Dakarun Kenya a wata fafatawa da su ka yi 'Yan kungiyar Al Shabab. Reuters
Talla

Mai Magana da yawun rundunar, Cyrus Oguna, yace sun kwace sansanin ba tare da wani tirjiya ba, sakamakon harin sama da na kasa da suka kaddamar, inda yace sun kwace tashar da misalin karfe biyun daren jiya.

Koda yake, ‘Yan tawayen da wasu mazauna yankin na ikrarin cewa har yanzu dakarun Kenyan na wajen garin ne.

Da yawa daga cikin mazauna yankin na Kismayo sun tabbatar da cewa, har yanzu dakarun na bakin teku, inda wani jirgin ruwa ya saukesu biye da wani jirgi mai tashin Angulu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.