Mutane 11 sun mutu a kisan ramuwar gayyar kasar Kenya
Akalla mutane 11 ne su ka mutu a kisan da wasu ‘Yan bindiga su ka yi wanda ake ganin na ramuwar gayyar ne na wasu mutane 52 da aka kashe a watan jiya.
Wallafawa ranar:
A cewar hukumar ba da agaji ta Red Cross, wasu mutane 10 kuma sun sami raunuka a harin wanda aka kai shi a yankin Tana River da ke kasar ta Kenya.
“Akwai tashin hankali sosai a yankin” inji wata jami’ar Red Cross, Nelly Muluku, a hirarsu da Kamfanin Dillancin labaran AFP.
A watan jiya ne aka kashe mutane 52 a wani rikicin ‘Yan kabilar Pokomo da Orma wadanda ke takaddama akan filaye da ruwa.
‘Yan kabilar Pokomo, dai mafi yawansu manoma ne da ke shuka kusa da tafki a yayin da su kuma ‘Yan Orma makiyaya ne.
A shekarar 2001, akalla mutane 130 aka kashe a rikici daba daban a yankin kuma tsakanin kabilun biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu