Isa ga babban shafi
Kenya

Manyan Jami'an Gwamnati Kenya da ake zargi zasu halarci Kotun Duniya

Yau Alhamis, ake saran uku daga cikin manyan jami’an Gwamnatin kasar Kenya, zasu gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifufuka, saboda zargin tinzira jama’a, wajen kashe kashen da aka yi a shekara ta 2007 da 2008 bayan zaben kasa baki daya.Mai Magana da yawun kotun, Jelena Vukasinovic, ta ce jami’an sun yi alkawarin halartar wannan zaman.Yau kuma ake saran fara wata shari’ar da 'yan kasar Kenya da suka gabatar, inda suke kalubalantar Gwamnatin Britaniya da cin zarafin 'yan kabilar Mau Mau, tsakanin shekarar 1952 da 1961, a karkashin mulkin mallaka.An dai tsare 'yan kabilar a wani sansanin Turawan, inda suka yi zargin an ci zarafin su, har ma da yiwa matansu fyade, inda suke bukatar biyar diyya. 

Carte / RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.