Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan harin kunar Bakin- Wake sun kashe mutum biyu a Najeria

Wasu hare - haren kunar Bakin – Wake da aka kai a ofisoshin ‘Yan Sanda ya yi sandiyar mutuwar mutane biyu a Jihar Sokoto da ke tarayyar Najeria. A wani harin na daban kuma an kai hari kan wasu ‘Yan Sanda dake tsaron gidan Mataimakin Shugaban kasar, Namadi Sambo, da ke garin Zaria wanda ya yi sanadiyar mutuwar farar hula daya.  

Ragowar wata mota da aka kai harin Kunar Bakin - Wake a cikinta a Najeriya
Ragowar wata mota da aka kai harin Kunar Bakin - Wake a cikinta a Najeriya Reuters/Stringer
Talla

Wani Jami’in bada hukumar Red Cross ya bayyanawa kamfanin Dillancin labaran faransa cewa harin na farko ya faru ne a ofishin ‘Yan Sanda da ke ‘Yan Marina kana na biyun ya faru ne a Unguwar Rogo, kuma duka ‘Yan kunar Bakin Wake su ka kai su.

Jami’in ya ce wani Dan Sanda da ‘Yar Sanda sun rasa rayukansu kana mutum 30 sun samu raunuka, mafi yawansu a kasuwar da ke kusa da ofishin ‘Yan Sandan.

Wani babban Jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce dan Kunar Bakin Waken ya doshi kofar shiga ofishin ‘Yan Sanda da mota inda ya ta da bama baman bayan an hana shiga ciki.

Wani mazaunin garin, Lawal Danfili wanda gidansa ke daura da inda abin ya faru ya bayyanawa Kamfanin Dillancin labaran AFP cewa, lokacin da mutane su ka ji karan bam din kowa sai ya zura gida a guje.

Ko da ya ke babu wani da ya fito ya dauki alhakin wannan hare-hare, a mafi yawan lokuta kungiyar Jama’atul Ahlil Sunnah lil Da’a wati Wal Jihad kan dauki alhakin irin wannan hare hare musamman akan jami’an tsaro.

Garin Sokoto shi ne fadar Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ta ke.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.