Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan fashi sun kashe mutane 26 a Jahar Zamfara a Najeriya

Wasu gungun ‘Yan fashi da makami a Najeriya, sun hallaka mutane 26 a wasu kauyuka biyu a Jahar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar. Jami’an tsaro sun ce ‘Yan bindigar sun bi gida-gida ne suna barin wuta.  

Taswirar Zamfara a arewacin Najeriya
Taswirar Zamfara a arewacin Najeriya Carte / RFI
Talla

Wani mazaunin garin Dangulbi, Ahmad Musa, ya shaidawa Rediyo Faransa cewa barayin sun kai harin ne a kauyen Dan Gulbi da Guru, kuma yace barayin adadin yawansu ya kai 100 kuma wadanda suka shigo kauyukan a saman Babura.

A cewar Malam Musa da misalain karfe 1:00 na daren Lahadi ne ‘Yan fashi suka abkawa mazauna kauyen Dan Gulbi sanye da bakaken kaya. Kuma nan take ne suka kashe mutane 18.

Rahotanni sun ce mutane da dama sun samu rauni sanadiyar harin na ‘Yan bidigar.

A watan Oktoban bara wasu ‘Yan bindiga sun taba kai hari a kauyen Lingyado a Jahar Zamfara inda suka kashe mutane 19 a wani hari da suka kai domin mayar da martanin kisan wani dan uwansu.

A watan Janairu ne kuma wasu ‘Yan fashi suka kai hari wata kasuwa kusa da jahar Katsina inda suka kashe mutane 15 tare da kona gawawwakinsu a karamar hukumar Birnin Magaji.

Najeriya dai tana fama da matsalar tsaro da tashin bama bamai musamman a Arewacin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.