Wasu ‘Yan Bindiga sun kai hari a Adamawan Najeriya
Wasu ‘Yan bindiga sun kai hari bom tare da musayar wuta a wani Ofishin ‘Yan Sanda a birnin Gulak da ke Adamawa arewa maso gabacin Najeriya a daren jiya alhamis kamar yadda kakakin ‘Yan sandan Jahar Nemuel Yoila ya shaidawa kamfanin Dillacin Labaran Faransa na AFP.
Wallafawa ranar:
Sai dai ‘Yan Sandan ba su tantance ko su wane ne ‘Yan Bindigar ba.
Wannan kuma na zuwa ne a dai dai lokacin da Sambo Dasuki Sabon mai ba shugaba Goodluck Shawara akan fannin Tsaro ya kai wata Ziyara a Jahar Yobe yankin da ke fama da hare haren bama bamai a Damaturu.
Wannan kuma ita ce ziyarar Kanal Sambo Dasuki ta Farko tun bayan nada shi sabon mai bai wa Shugaban kasa shawara.
Kanal Dasuki ya nemi hadin kai daga Sarakunan gargajiya domin taimakawa wajen fito da hanyoyin kawo karshen jubar da jini a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu