Isa ga babban shafi
Equatorial Guinea

Shugaban Equatorial Guinea ya nada ‘yayansa manyan mukaman gwamnati

Shugaban Kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema, ya nada ‘ya’yansa biyu da kuma kaninsa a sabuwar gwamnatin kasar bayan ya nada Vincente Ehate Tomi mastsayin Fira Minista.

Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo
Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo Reuters/James Akena
Talla

Cikin mutane 55 da aka nada a cikin sabuwar gwamnatin Nguema, 12 daga cikinsu ‘Yan’uwan ne ga shugaban, da suka hada da kanin sa Mba Nguema, a matsayin Ministan tsaro da Dan sa Gabriel Nguema, a matsayin Ministan makamashi da masana’antu.

Kuma cikin ‘yayansa, Milam Nguema, ya karbi mukamin Fira Minista.

Obiang wanda shi ne shugaban da ya fi kowa dadewa kan karagar mulki a Afrika ya sake nada dansa Teodorin a matsayin mataimakin shugaban kasa na biyu domin kula da sha’anin tsaro.

‘Yan adawa dai a kasar sun ce shugaban yana neman ya mika mulki ne ga ‘yayansa.

A shekarar 1979 ne Mista Obiang ya karbi shugabancin Equatorial Guinea bayan samun nasarar juyin Mulki.

Babu wani bayani cikakke game da lokacin da wa’adin Obiang zai kawo karshe a Sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi a watan Nuwamba.

Karkashin sabon kundin tsarin mulkin ne aka amince da samun mataimakin shugaban kasa guda biyu.

Kasar Equatorial Guinea tana cikin kasashen Afrika masu arzikin Man Fetir amma al’ummar kasar suna cikin matsanancin halin talauci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.