Isa ga babban shafi
Niger

Hama Amadou shugaban majalasar dokokin a jumhuriyar ta 7 ta Nijar

Hama Amdou tsohon Praministan kasar jumhuriyar Nijar daga shekara ta 2000 zuwa ta 2007 a karkashen jagorencin tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja,bayan zabe a majalasar dokokin kasar ta Nijar ,ya kassance zababen shugaban majalasa dokokin kasar ta farko a jumhuriya ta 7 a kasar ta Nijar.Yan majalasa guda 103 ne su ka amunce da shi, a yayin da guda daya ya ki amuncewa da zaben.Jama’iyar da ya ke jagorenta ta MODEN na da ‘yan majalasa guda 23 a zauren.Hama Amadou na da shekaru 60 a duniya da kuma ya kassance shi daya ne dan takarar kujerar majalasar.Har yanzu dai jama’ar kasar Nijar, da ta duniya ,ta zura iddo tare da kashe kunnuwa ta na jira da ganin tare da jin sunayen sabin mambobin gwamnatin farko a jumhuriya ta 7 da Praminista Brigi Rafini zai jagorenta. 

Hama Amadou sabon zababen shugaban majalasar dokokin ta jumhuriya ta 7 a kasar Nijar
Hama Amadou sabon zababen shugaban majalasar dokokin ta jumhuriya ta 7 a kasar Nijar
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.