Isa ga babban shafi
Equatorial Guinea

Kasar Equatorial Guinea ta kashe hafsoshin soji hudu

Kungiyar kare Hakkin Bil Adama, ta Amnesty International, ta zargi Gwamnatin kasar Equatorial Guinea, da kashe hasoshin sojin kasar hudu, saboda zargin kai hari fadar shugaban kasar bara.Daraktan kungiyar, mai kula da nahiyar Afrika, Erwin van der Borght, yace an kashe hafsoshin ne, bayan an gudanar musu da wata shari’ar da babu adalci a ciki.Kungiyar tace, an kamo wadanan hafsoshi ne daga kasar Janhuriyar Benin, a watan Janairu, inda suke gudun hijira dan yi musu shari’a.Wadanan sojoji sun hada da Jose Abeso Nsue, Manuel Ndong Anseme, Jacinto Micha Obiang da Alipio Ndong Asumu.Kasar Equatorial Guinea, nada daga cikin kasashen da aka fi samun cin hanci da rashawa, inda rahotan kungiyar dake sa ido ta Amnesty International ya sanya ta a matsayi na 12 daga kasa, a cikinkasashe 180 na duniya. 

Malabo, Kasar Equatorial Guinea
Malabo, Kasar Equatorial Guinea Flickr/ John Kots
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.