Isa ga babban shafi
Congo Brazzaville

Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutane 50

Wani jirgin kasa da ya kauce bisa kan layi, ya hallaka kusan mutane 50, a kasar Congo Brazzaville, kamar yadda kamfanin jirgin kasr, na kasar ya bayyana yau Talata.An garzaya wadanda suka jikata zuwa asibiti bayan faruwar hadarin.Hadarin ya faru cikin daren jiya Litinin, yayin da jirgin ya fito garin Pointe-Noire, inda aka samu munanan hadarukan cikin shekarun da suka gabata.Hadarin ya faru kimanin kilo mita 60 kusa da tashen jiragen kasa garin Yanga, dake yankin na Pointe-Noire.Akalla mutane 50 sun hallaka cikin hadari da ya faru a wannan yankin cikin shekara ta 2001, inda yawanci suka kone.

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.