Isa ga babban shafi
Amurka-Iraqi

IS: Amurka za ta ba kabilun Iraqi makamai

Kasar Amurka tace zata ba kabilun Iraqi mabiya Sunni makamai domin yakar Mayakan IS da suka mamaye yankin arewacin kasar. Amurka tace zata kashe makudan daloli domin taimakawa mutanen kasar Iraqi su kare kansu bayan tura kwararru domin horas da su.

Mayakan IS da ke da'awar jihadi a Iraqi da Syria
Mayakan IS da ke da'awar jihadi a Iraqi da Syria REUTERS
Talla

Gwamnatin Barack Obama tace zata ba kabilun Iraqi makamai musamman mabiya Sunni a lardin Anbar domin yakar Mayakan IS da ke barazana a yankin.

Irin Makaman da Amurka tace zata ba Mutanen na Iraqi sun hada da Bindiga kirar AK 47 hadi da rokoki da gurneti.

Mayakan IS  da ke da'awar Jihadi  sun kwace garuruwa da dama a Iraqi da Syria kuma Amurka tana ganin ba kabilun na Iraqi makami domin kare kansu ya dace.

Sai dai kuma Amurka za ta ba kabilun na Iraqi makamai ne ta hannun gwamnatin kasar.
A jiya Lahadi Mayakan Kurdawa 20 ne rahotanni suka ce an kashe a musayar wutar da suka yi da Mayakan IS domin kwace yankin Diyala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.