Isa ga babban shafi
IS-Amurka

IS ta sake fille kan wani Ba’amurke

Kungiyar Mayakan ISIS ta fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda ta fille kan wani ma’aikacin agaji Dan kasar Amurka Peter Kassig, a matsayin gargadi ga kasar kan shirin girke sojojinta a cikin kasar Iraqi. Shugaba Obama na Amurka ya la’anci kisan Ba’amurken.

Abdul-Rahman "Peter" Kassig, da Mayakan IS na Iraqi suka kashe
Abdul-Rahman "Peter" Kassig, da Mayakan IS na Iraqi suka kashe REUTERS/Kassig Family/Handout
Talla

Bidiyon ya nuna yadda aka fille kan mutane 18 da kungiyar ta bayyanasu a matsayin sojojin kasar Syria.

Amurka tace tana nazari domin tantance bidiyon kamar yadda Bernadette Mehan, mai magana da yawun Hukumar tsaron kasar ta bayyana.

An sace Kassiq ne a inda ya ke aikin hidima da ‘Yan gudun hijirar Syria, kuma shi ne bature na biyar da Mayakan IS suka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.