Isa ga babban shafi
Thailand

Gwamnatin Sojin Thailand ta sauya dokar Kasar

Gwamnatin sojin Thailand, ta sauya dokar Soji, inda ta maye gurbinta da saban tsari, yayin da, ba ta yi gyran fuska ba, a sashin da ya baiwa Sojoji karfi a kundin tsarin mulkin Kasar na wucen gadi, da kungoyoyin kare hakkin dan adam na Kasar suka caccaka

Sojojin Thailand
Sojojin Thailand REUTERS/Chaiwat Subprasom
Talla

Tsarin dokar samar da tsaro zai cigaba da tabbata kamar yadda yake, inda aka haramta taron siyasa na jama’ar da yawansu ya zarce biyar, lamarin da ya sa ‘yan kasar ke ganin cewa tawaye ce ga wasu hakkokinsu.

Kuma tun lokacin da gwamnatin ta fitar da dokar sojin, bayan ta kwace mulki daga hannun zababben gwamantin kasar a watan mayun bara, al-ummar kasar ke fuskantar matsalar tauye hakkokinsu.

Wata sanarwa da aka fitar a kafar talabijin na gwamnati, ta bayyana cewa, sauye dokar sojin na zuwa ne sakamakon umarni daga masarautar kasar, kuma kwana daya da ganawar da shugaban Soji kuma firaministan kasar Prayut Chan O Cha , ya yi da sarki Bhumibol da ke jinya, inda ya nemi izinin Sarkin dangane da sauya dokar da ake ta cecekuce a kai.

Dokar sojin kasar dai, ta baiwa sojoji damar gurfanar da duk wanda ya yi barazana ga tsaron kasar ko kuma ya ci zarafin masarauta kasar ta Thailand.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.