Thailand
Chan-ocha ne sabon Firaministan Thailand
Majalisar Kasar Thailand da sojoji suka nada bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Yingluck Shinwatra ta zabi shugaban sojin kasar Janar Prayut Chan-O-Cha a matsayin sabon Firaminista. A kuri’ar da aka gudanar a Majalisar da Prayut shi kadai ya tsaya zaben, ya samu kuri’u 191 daga cikin Majalisar mai wakilai 197.
Wallafawa ranar:
Talla
Gwamnatin Sojin ta yi watsi da shirin gudanar da zabe a watan Oktoba domin dawo da kasar a mulkin dimokuradiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu