Isa ga babban shafi
Singapore

Singapore Na Zaman Makoki Saboda mutuwar Fira Minista Na Farko

Shugabannin kasashen duniya na ta aikewa da sakonnin taaziyya ga Gwamnatin kasar Singapore sakamakon mutuwar PM kasar na farko Lee Kuan Yew mai shekaru 91 wanda shine jagoran dukkan arzikin da kasar ta samu yanzu.Shugaban Amirka Barack Obama ya fadi cikin ta'aziyyar sa cewa marigayin mai hangen nesa ne, wanda ya yi hankoron ganin Singapore ta kai ga nasarorin da ta samu yanzu haka.Suma dai tsoffin shugabannin kasar Amirkan George W Bush da mahaifin sa George H W duk sun jinjinawa marigyin saboda jajircewar sa wajen ganin Singapore ta kafu sosai.Hukumomin kasar ta Singapore sun bayyana zaman makoki na tsawon mako daya.  

Marigayi tsohon Fira Minista Lee Kuan Yew
Marigayi tsohon Fira Minista Lee Kuan Yew REUTERS/Edgar Su/Files
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.