Isa ga babban shafi
Masar

Talata Za'a Yankewa Tsohon Shugaban Masar Morsi Hukunci

A Jibi Talata idan Allah ya kaimu ne wata kotu a kasar Masar za ta zartas da hukuncin farko kan tsohon shugaban kasar  Mohammed Morsi gameda zargin hannu wajen rasa rayukan masu bore a zamanin sa.Hukuncin wadda za ta kasance ta farko cikin shariar da ake yi masa tun bayan kawar dashi daga madafun iko, ana ganin watakila hukuncin kisan za'a zartas masa.Bayaga zartas da hukunci na jibi, ranar 16 ga watan gobe akwai zartas masa da hukunci har biyu da wata kotun za tayi.  

Tsohon Shugaba Mohammed Morsi cikin kotu yana sauraren sharia
Tsohon Shugaba Mohammed Morsi cikin kotu yana sauraren sharia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.