Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Amurka ta nuna shakka game da kashe jagoran Boko Haram

Kasar Amurka ta bayyana shakkunta a game da ikirarin da ma’aikatar tsaron Najeriya ta yi na kashe wani da ke bayyana kansa a matsayin Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram.

John Kerry, Sakataren Wajen Amurka.
John Kerry, Sakataren Wajen Amurka. REUTERS/Brendan Smialowski
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry wanda ke zantawa da manema labarai a gefen taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ya ce Amurka ba ta daukar wannan ikirari da muhimmanci, kuma yanzu haka suna aiki tukuru domin tabbatar da gaskiyar labarin.

Ita dai rundunar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta kashe wani mutum mai suna Bashir Abubakar wanda ke bayyana kansa a fayafayin bidiyo a matsayin Abubakar Shekau jagoran wannan kungiya da ta kashe dubban mutane a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.