Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta harbe Dan Obasanjo

Mayakan Kungiyar Boko Haram a tarayyar Najeriya, sun harbe Dan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Lt. Col. Adeboye Obasanjo a Kafa, sai dai ba’a ce ya mutu ba

nigerianmonitor.com
Talla

Adeboye dai na a Runduna ta 3 ne da ke a jihar Filato, kuma an harbe shi ne lokacin da Dakarun Najeriya suka kwashe Sa’o’i 12 suna dauki-ba-dadi tsakaninsu da Mayakan Boko Haram da yanzu haka ke ci gaba da kama kauyuka a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

‘Yan boko Haram din dai sun yiwa Sojin Najeriyar Kofar Rago ne, inda a nan ne suka samu sa’ar harbe Dan tsohon shugaban kasar a Kafa.

Ance dai dukkanin bangarorin Biyu sun ji jiki a wannan fadan da ake, kuma ya zuwa yanzu dukkanin masu magana da Yawun Dakarun Najeriya sun kashe Wayoyinsu, abinda ya hana samun cikakken bayani kan wannan al’amari.

Rundunar Sojin Najeriyar dai na can tana jibge Dakarunta a Michika inda ‘yan Boko Haram suka kafa sansani, a yayin da Jiragen yaki keta aman Wuta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.