Isa ga babban shafi

Chiellini ya yi ritaya daga kwallo bayan shafe shekaru 23 ya na taka leda

Ma tsaron baya na Italiya da ke taka leda da Juventus Giorgio Chiellini ya sanar da rataye takalmansa daga fagen tamaula gabaki daya, yayinda ya bayyana rayuwarsa ta kwallo mai cike da kayatarwa har zuwa ranar karshe.

Chiellini yayin taka leda a Juventus.
Chiellini yayin taka leda a Juventus. AFP/File
Talla

Chiellini mai shekaru 39 wanda ya jagoranci tawagar Italiya a matsayin kyaftin wajen lashe kofin Euro 2020 bayan doke Ingila a filin wasa na Wembley, a jiya ne ya sanar da wannan mataki wanda ke kawo karshen shekaru 23 da ya shafe ya na taka leda.

Chiellini wanda ya yi suna da Juventus, a bara ne ya koma Lig din Amurka da taka leda karkashin kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles FC, kungiyar da ta sha kaye a hannun Columbus a Asabar din nan yayin wasan karshe na cin kofin Lig.

Dan wasan na Italiya ya sanar da wannan mataki ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na X inda ya godewa dimbin magoya baya wadanda ya ce da taimakonsu ne ya kai inda ya ke.

A shekarar 2000 ne Chiellini ya faro kwallo da kungiyar kwallon kafa ta Livorno gabanin gina kanshi a gasar Seria A tare da zama cikin zakakuran da suka taka leda a lig din.

Chiellini ya lashe kofunan Seria A har guda 9 a jere ga Juventus daga shekarar 2011 zuwa 2020 sai kuma Coppa Italia har guda 5.

A shekarar 2022 ya yi ritaya daga dokawa kasar shi Italiya kwallo bayan haskawa a wasanni 117 tare da zura kwallaye 8.

Wani sakon girmama da Juventus ta wallafa a shafinta bayan sanarwar tsohon dan wasan na ta, ta ce domin girmama magoya bayan Juventus da kakar wasa 17 da dan wasan ya shafe ya na taka leda, riga mai lamba 3 za ta ci gaba da kasancewa a kungiyar domin Chiellini kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.