Isa ga babban shafi
wasanni - Europa League

Mourinho ya sha kashi mafi muni a rayuwarsa ta koci bayan doke Roma

Jose Mourinho ya sha kayi mafi muni a tarihin aikinsa na horas wa, bayan da Roma ta sha kashi a hannun Bodo/Glimt da ci 6-1 a gasar Europa League.

Kocin Roma Jose Mourinho lokacin da yake baiwa 'yan wasansa shawara yayin wata wasa 12/09/21.
Kocin Roma Jose Mourinho lokacin da yake baiwa 'yan wasansa shawara yayin wata wasa 12/09/21. Vincenzo PINTO AFP/Archives
Talla

A daren da Tottenham ta sha kashi a hannun Vitesse, da ci 1 – 0 tsohon kocin Spurs din Jose Mourinho ya shiga  mawuyacin lokaci.

Ana wasa ci 2-1 kafin atafi hutun rabin lokaci, amma kawai sai lamari ya sauya tare da bada mamaki bayan dawowa daga hutu, duk da sauye-sauyen ‘yan wasa har sau 5 da Mourinho yayi, amma sai da akayi musu dukar kawo wuka har 6-1.

Wannan ne karon farko da wata kungiya da Mourinho ke jagoranta ta sha ruwan kwallaye har 6 ko sama da haka a wasa guda, a wasanni 1,0008 na rayuwarsa ta koci.

Kafin wannan lokaci rashin nasarar mafi muni shine lokacin da Barcelona ta yi musu kacha-kacha da ci 5-0 a shekarar 2010 lokacin yana jagorantar Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.