Kungiyoyi zasu gabatar da 'yan wasa 26 a gasar nahiyar Turai ta bana
Hukumar shirya gasannin kwallon kafar Turai ta dan yi sauyi kan yawan adadin ‘yan wasa da zasu shiga tawagogin gasar neman cin kofin nahiyar ta wannan shekara.
Wallafawa ranar:
Sabon tsarin UEFA ya baiwa Kowacce tawagar kwallon kafa da za ta buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, damar zuwa da 'yan wasa 26, maimakon 23 da aka saba a baya.
Hukumar ta yi wannan sauyin ne don ragewa ‘yan wasa gajiya bayan buga wa kungiyoyinsu wasanni kusa da juna, sakamakon bullar cutar korona.
Matakin zai taimakawa masu horar da tawagogin samun saukin zabin 'yan wasa koda annobar ta shafi wata tawaga.
An kuma amince kowacce tawaga ta sauya 'yan wasa biyar-biyar a kowacce karawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu