Isa ga babban shafi
Wasanni

Gasar Europa: An fitar Everton a matakin rukuni

Kungiyar Everton ta gaza kai wa zagaye na gaba gasar Europa, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Lyon daga kasar Faransa da kwallaye 3-0.

Mai horar da kungiyar Everton na wucin gadi David Unsworth.
Mai horar da kungiyar Everton na wucin gadi David Unsworth. Reuters / Craig Brough Livepic
Talla

A wasan farko da suka fafata, har gida Lyon samu nasara kan Everton da kwallaye 2-1. Hakan yasa Everton ta fice daga gasar ta Europa duk da cewa akwai sauran wasanni 2 da zata buga.

Rashin nasarar ya sake jefa jagorancin horar da kungiyar cikin tsaka mai wuya mai barazanar maida murnar mai rikon horar da kungiyar David Unsworth ciki, dangane da fatansa na ganin ya rike mukamin akan cikakkiyar yarjejeniya.

Har yanzu dai Everton na kokarin dagowa daga ajin ‘yan dagaji a gasar Premier, sakamakon rashin nasarar da kungiyar ta rika fuskanta a jere a wasannin gida da na waje, wanda hakan yasa aka kori mai horar da ita a makon da ya gabata, Ronald Koeman, bayanda Arsenal ta lallasa su da kwallaye 5-2 a gasar Premier.

A kakar wasa ta bana, akalla fan miliyan £150, kungiyar ta Everton ta kashe domin sayen sabbin 'yan wasa, sai dai duk da haka kwalliya bata fara biyan kudin Sabulu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.