Isa ga babban shafi

Gasar Europa ta dawo daga hutun Korona

Yau ake dawowa wasannin gasar Kwallon kafa ta Europa, domin karasa wasannin matakin da ya kunshi kungiyoyi 16, bayan hutun dole da annobar korona ta sa aka dakatar da gasar.

Kofin gasar Europa
Kofin gasar Europa Reuters
Talla

Tsakanin yau Laraba da gobe Alhamis za’a karkare zageyen na ‘yan 16, zagaye na biyu, wanda tun a watan Maris aka fafata wasannin zagaye na farko kafin a dakatar da wasannin saboda korona.

Cikin kungiyoyin da zasu fafatawa wasannin na yau da gobe, harda Manchester United da Wolves da Rangers da Inter Milan da kuma Roma.

Bari mu duba jadawalin kungiyoyin da zasu hadu a wasannin.

Da misalin 5 : 55 pm: FC Copen-hagen v Istanbul Basaksehir (1 - 0 a wasan zageye na farko)

Yayin da Shakhtar Donetsk v Wolfsburg (  2-1 wasan farko) .

Sai kuma da misalin karfe 8pm agogon: Inter Milan v Getafe (kuma tun farko basu yi wasa zaye na farko ba)

Yayin da Manchester United v Lask (  5-0 zageyen farko ) .

Sai kuma wasannin da za’a fafata gobe Alhamis, 6 ga wata idan Allah ya so.

Bayer Leverkusen v Rangers zasu fafata da misalin karfe 5:55pm(  3-1 wasan farko)

Yayin da Sevilla v Roma.(an dage wasansu na farko)

Basel v Eintracht Frankfurt da karfe 8pm ( 3-0 wasan farko)

Sai kuma WOLVES v Olympiakos (wanda sukayi canjarasa 1-1 farkon).

*wasa tsakanin Inter Milan v Getafe da kuma Sevilla v Roma, shine wasan sun a farko a zageyen na 16, saboda dage wasannin na farko da akayi saboda koronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.