Barca ta doke PSG, Bayern ta sha kashi a gidan Porto
FC Barcelona ta bi Paris Saint-Germain har gida ta doke ta 3 da 1 a karawar farko zagayen kwata fainal da suka fafata a gasar zakarun Turai a Paris. Neymar ne ya fara jefa wa Barcelona kallo a raga ana minti 18 da fara wasa, yayin da kuma Suarez ya jefa sauran kwallayen guda biyu a ragar PSG.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu Barcelona ta karya lagon PSG na buga wasanni a gasar Turai 34 ba tare da an samu galabarta ba tun a 2006.
A ranar Talata makon gobe ne PSG za ta kai wa Barcelona ziyara inda zata nemi rama kwallayenta.
A kaka biyu da suka gabata a irin wannan zangon ne ake korar PSG a gasar, kuma ana korar ta ne da yawan kwallayen da aka zira a gidanta.
A daya bangaren FC Porto ta doke Bayern Munich ne 3 da 1 a karawa ta farko da suka fafata a gidan Porto kasar Portugal.
Sakamakon wasan na nuna Porto ta sa kafa guda a zagayen dab da na karshe kafin haduwa ta biyu, ko da ya ke Bayerm ta jefa kwallo guda a ragarta.
Porto dai na fatar tsallake wa zagayen dab da na karshe ne a zagayen farko tun a 2004 da Mourinho ya lashewa kungiyar kofin gasar zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu