Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Atletico ta rike Real, Juve ta doke Monaco

Wasa tsakanin Atletico Madrid da Real Madrid an tashi ne babu ci a fafatawar da kungiyoyin biyu ‘yan gari guda suka yi a gasar zakarun Turai a gidan Atletico. Real da Atletico za su sake gumurzu a Bernabeu gidan Real Madrid a mako mai zuwa inda za a tantance gwani daga cikinsu.

Mario Suarez na Atletico yana gumurzu da Cristiano Ronaldo  na Real Madrid
Mario Suarez na Atletico yana gumurzu da Cristiano Ronaldo na Real Madrid REUTERS/Sergio Perez
Talla

A karawar jiya Real Madrid ta kai hare hare amma gwalkifan Atletico yana kabe kwallayen.

Akwai dai ‘yan wasan Atletico da suka zargi mutumin kasar Serbia wanda ya yi alkalancin wasan.

Alkalin ya haramta wa Atletico fanariti a lokacin da Ramos ya tare Torres bayan ya yanke shi.

Mario Suarez na Atletico wanda alkalin Milorad Mazic ya haramtawa buga wasa na biyu, ya ce bai kamata hukumar kwallon Turai ta ba shi alkalancin babban wasa irin wannan ba.

Sai dai kuma hukumar EUFA na iya daukar mataki akan kalaman na Suarez.

Karo na bakwai ke nan Real Madrid na kokarin samun galaba akan Atletico a bana.

Karo na hudu kuma ke nan da Real Madrid ta gaza jefa kwallo a gidan Atletico a bana.

A ranar 22 ga watan Afrilu ne kungiyoyin biyu za su sake haduwa karo na 8 a Santiago Bernabeu.

Juve vs Monaco

Dan kasar Chile Arturo Vidal ne ya jefa wa Juventus kwallo guda a ragar Monaco a fafatawar da suka yi a Italiya, kafin su sake kece raini a Faransa.

Dan wasan na Chile ya jefa kwallon ne a raga a bugun fanariti da alkawalin wasa ya ba Juventus bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Dan wasan Monaco Berbatov ya ce za su rama a karawarsu ta biyu.

PSG vs Barca, Porto vs Bayern Munich

Paris Saint-Germain za ta karbi bakuncin Barcelona a yau Laraba, a lokaci guda ne kuma Bayern Munich zata fafata da FC Porto.

Koca-kocan kungiyoyin biyu dukkaninsu tsofin ‘yan wasan Barcelona ne wadanda suka yi wasa tare.

Pep Guardiola na Bayern Munich zai hadu ne da abokin wasansa Lopetegui wadanda suka taka kwallo tare shekaru 20 da suka gabata a Barcelona.

A bana babu kungiyar da ta doke Porto a gasar zakarun Turai, akan haka masu sharhi na ganin sai Bayern ta yi gaske.

Akwai manyan ‘yan wasan Bayern Munich da ke jinya da suka hada da Arjen Robben da Franck Ribery da Bastian Schweinsteiger.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.