Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Real Madrid ta sha da kyar

Real Madrid ta sha kashi a hannun Schalke 04 a jiya kodayake ta tsallake zuwa zagaye na gaba a gasar zakarun Turai saboda yawan kwallayenta a gidan Schalke, Amma batun shan kashin ne ya mamaye kanun labaran jaridun wasanni a Turai musamman ma Spain.

Magoya bayan  Real Madrid
Magoya bayan Real Madrid REUTERS/Youssef Boudlal
Talla

Schalke ta ba Real kashi ci 4 da 3 amma Real ta tsallake saboda kwallaye biyu da ta zira a ragar Schalke a karawa ta farko.

Jaridar Wasanni ta AS da ake bugawa a birnin Madrid, ta ce Real Madrid ta tsallake zuwa kwata Fainal cikin kunya.

Jaridar Marca kuma da ke goyon bayan kungiyar ta yi sharhi ne akan irin tsoratarwar da wasan jiya ya haifar a Bernabeu gidan Madrid.

Batun tarihin da Ronaldo ya kafa a Turai a wasan na jiya ya ja hankalin jaridu da dama.
Jaridar Marca tace ribar da aka samu a wasan shi ne tarihin da Ronaldo ya kafa a matsayin limamin raga da kwallaye 78, wanda ya ba shi damar shan gaban Raul tare da yin kafada da Messi abokin adawarsa na Barcelona da jimillar kwallaye 75 a gasar zakarun Turai.

Kwallaye biyu Ronaldo ya jefa a raga a jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.