Chelsea ta ba City tazarar maki biyar
Chelsea da ke saman teburin Premier ta doke West Ham United ci 1 da 0, wanda ya ba ta damar ci gaba da jagorancin teburin gasar da tazarar maki 5. A filin Etihad Manchester City ta ba Leicester kashi ne ci 2 da 0.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Manchester United ta doke Nwcastle United ci 1 da 0, ana saura minti guda a kammala wasa Young ya jefa wa Manchester kwallonta a raga.
Arsenal ta doke QPR ne ci 2 da 1, kuma yanzu Arsenal ta haye saman Manchester United a matsayi na uku a teburin Premier.
Liverpool ta lallasa Burnley ci 2 da 0. Stoke City ta doke Everton ci 2 da 0. Swansea ta sha kashi ne a hannun Tottenham.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu