Isa ga babban shafi
Premier League

Ba na fuskantar matsin lamba-Pellegrini

Kocin City Manuel Pellegrnin ya yi watsi da rahotannin da ke cewa yana fuskantar matsin lamba bayan City ta kashi a hannun Barcelona a zakarun Turai tare da shan kashi a hannun Liverpool a Premier. Pellegrini yace City ba ta dauko shi ba don ya lashe mata kofi duk shekara.

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini
Kocin Manchester City Manuel Pellegrini REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Tazarar maki biyar ne Chelsea ta ba City mai rike kofin gasar Premier. Idan kuma Manchester City na son matsawa Chelsea a teburin gasar ya zama wajibi ta lashe wasanta a gida da zata fafata a yau Laraba da Leicester.

Pep Guardiola na Bayern Munich ya yi watsi da jta jitar da ake yadawa cewa zai karbi aikin horar da Manchester City a karshen kaka.

Tsohon kocin na Barcelona ya ce babu wata tattaunawa tsakanin shi da City kuma baya neman a tuntube shi.

Wasannin Premier a yau Laraba.

Chelsea ta ke jagorancin teburin Premier za ta fafata ne da West Ham a yau Laraba bayan ta kammala bikin lashe kofin Carling a karshen mako.

Manchester United kuma za ta kai wa Newcastle United ziyara ne yayin da kuma QPR za ta karbi bakuncin Arsenal.

Liverpool za ta kara ne da Burnley.

Wasannin Talata

A jiya Southampton ta hauro zuwa matsayi na biyar a teburin premier bayan ta samu sa’ar Crystal Palace ci 1 da 0.

Aston Villa ta sha da kyar ne a hannun West Brom ci 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.