Isa ga babban shafi
FIFA

Kotun wasanni ta yi watsi da koken Barcelona

Kotun wasanni CAS ta amince da haramcin sayen ‘yan wasa na tsawon shekara guda akan Barcelona bayan kungiyar ta kalubalanci hukuncin da FIFA ta yanke akanta a watan Afrilu. Kotun ta fadi a cikin wata sanarwa cewa ta yi watsi da koken Barcelona saboda ta keta dokar cinikin ‘yan wasa ‘yan kasa da shekaru 18.

Barcelona ta sha kashi a gidan Real Madrid ci 3 da 1
Barcelona ta sha kashi a gidan Real Madrid ci 3 da 1 REUTERS/Juan Medina
Talla

Haramcin sayen ‘yan wasan zai fara aiki a farko watan Janairu har zuwa karshen kakar 2015 zuwa 2016. Hakan na nufin Barcelona ba za ta saye dan wasa ba har sai zuwa 2016.

Baya ga hukuncin, FIFA ta ci tarar Barcelona kudi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.